Karatu a kasar Denmark
Kasar denmark na daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya,hakan ne yasa suke bada damar yin karatu a kasar kyauta ga kasashe masu tasowa,wadda wata babbar jami’a a kudancin kasar ta Denmark take bayarwa,tareda tallafawar babbar hukumar ilimi da kimiyya ta gwamnatin tarayyar kasar,ga wasu kayadaddun dalibai,wadanda zasu samu kyakykyawar kulawa da kuma tallafi a duk shekarunsu na karatu har zuwa kammalawa.
Ita wannan scholarship din tana dauke da bangarori biyu ne: akwai bangaren biyan cikakken kudin karatu [full tuition fee] da kuma tallafi [grant].Sannan wannan scholarship ana bada tane ga daliban da suke da hazaka,wadda hakan na nufin ya danganta da makin da dalibi ya samu lokacin karatunsa na digiri na farko wato grade point average.
A takaice:
- kasa: Denmark
- Wurin Karatu: Karatu a kasashen afirka | Karatu a kasashen Asia | Karatu a kasar Australia | Karatu a kasar Canada | Karatu a kasashen Europe | Karatu a kasar USA
- Nau’in Karatu: Secondary School Scholarships | Undergraduate scholarships | Postgraduate scholarships | Masters Scholarships | PhD Scholarships | Competitions | Internships | Training | Fellowships
- Reward: Cikakkiyar scholarship | Tallafi [Grant] da biyan DKK dubu uku kowane wata
- Lokacin Rufewa: Daya ga watan fabrairu shekarar dubu biyu da ashirin da biyu: February 1,2022
Wannan scholarship din me suna Danish Government Scholarship ta kasar Denmark suna bada tallafin karatu,ko dai su biya gaba daya ko kuma a biya wani bangare na karatun dalibi,suna biyan kudin daya zama wajibi dalibi ya biyasu a makaranta,amma baya da wannan babu wani tallafi daza su bawa dalibi kamar biyan kudin abinci,kudin kashewa da sauran kananan abubuwan bukatu na yau da kullum.
Abubuwan da scholarship din take bukata:
Dole ne dalibi yazama ya fito daga yankin daba na turai ba [non-EU/EEA] ma’ana kasashen dasuke bana turai ba,sannan ya nemi daya daga cikin wadannan kwasa kwasai na engineering a Sonderborg [programme start in autumn] kuma ya biya kudin makarantar
- MSc in Engineering - Mechatronics-
- MSc in Engineering - Electronics [Sonderborg]
Bugu da kari wannan scholarship din kadai ga daliban da suka cancantane,kuma daliban da suka samu offer ta karatu to tabbas zai samu scholarship din.
Amma bangaren Engineering yafi yiyiwar samun wannan tallafin.
Sannan duk wadda ya samu Danish State Grant,to bazai samu wannan scholarship ba.
Lokutan Scholarship din:
Kamar yadda aka fada a baya wannan scholarship tana dauke ne da bangare guda biyu:
- Akwai biyan cikakken kudin makaranta [full tuition]
- Akwai kuma tallafi [grant]
Takardun da ake bukata:
Domin zama cikakken dalibi ya zama wajibi duk wadansu takardu da ake da bukata sun zama a shirye kafin lokacin rufewa,domin tantancewa.
Suna da bukatar:
- Transcript na karatun digiri da kuma diploma a kasar ingila,Danish,Swedish ko Norway -kuma dole ya kunshi jerin makin da dalibi ya samu a kowane kwas.
- Gabatar da jerin kwasa kwasan da dalibi ya karanta a cikin transcript
- Shaidar kwarewa a yaren turanci
Ga link din:
.