📱 Yadda Zaka Dauki Video Ko Screen Recording Ko Da Wayarka A Kashe Take!
Shin ka taba son daukar bidiyon wani abu cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba? Ko kuma kana son yin recording din abinda ke faruwa a screen din wayarka amma ba ka son hasken wayar ya rinka ci?
To, ga mafita! Akwai wani babban application mai suna CameraBR (Background Recorder) wanda aka kera shi musamman domin daukar hoto, bidiyo, ko yin recording din screen koda kuwa ka danna maballin "Power" ka kashe fuskar wayar (Screen off).
🌟 Menene Amfanin Wannan Application Din?
Wannan manhajja tana da amfani sosai a wurare daban-daban, musamman idan ana maganar tsaro ko adana bayanai:
Daukar Bidiyo a Boye: Zaka iya fara recording sannan ka kashe screen din wayar ka saka ta a aljihu ko ka ijiye ta akan tebur, zata ci gaba da daukar bidiyo ba tare da kowa ya sani ba.
Ajiye Batir: Idan kana son yin dogon recording (kamar taro ko lecture), kashe screen din yana taimakawa wajen rage cin batir.
Tsaro: Zaka iya amfani da shi wajen gano abinda ke faruwa a kusa da kai idan baka nan, muddin ka saita shi yadda ya kamata.
Screen Recording: Yana daukar duk abinda kake yi a wayarka ba tare da alamar recording din ta fito fili ba.
🛠 Yadda Zaka Morishi (Matakan Amfani)
Idan kana son ka kware wajen amfani da wannan app din, ga yadda zaka yi:
Saukewa (Download): Jeka Google Play Store sannan ka bincika "Background Video Recorder" ko "CameraBR".
Saitin Sirri (Settings): Bayan ka bude shi, shiga bangaren Settings domin saita wace kyamara kake son amfani da ita (ta gaba ko ta baya) da kuma ingancin bidiyon (Quality).
Saita Lokaci (Schedule): Daya daga cikin abubuwan ban mamaki shine zaka iya saita lokaci (Timer). Misali, zaka iya saita shi ya fara recording da kansa da misalin karfe 2:00 na rana koda baka taba wayar ba.
Boye Bidiyo (Gallery Hide): Tabbatar ka kunna fasalin boye bidiyon daga cikin babban gallery din wayarka domin sirrinka ya kasance a boye.
Fara Amfani: Danna maballin Start. Daga nan zaka iya kashe screen din wayar ka ko ka fita ka shiga wani app din daban (kamar WhatsApp), recording din zai ci gaba a fake.
MUHIMMI: Ana amfani da wannan manhajja ne don dalilai na ilimi, tsaro, ko bukatar kai. Don Allah kar a yi amfani da shi ta hanyar da zata ci zarafin sirrin wasu mutane ba tare da izininsu ba
For Download : Click Here
