Yadda Ake Samun Kudi Ta Whop Ta Amfani da Video da Social Media
A yanzu akwai sabuwar hanya da mutane da dama suke amfani da ita wajen samun kudi online ba tare da sun kirkiro content daga farko ba. Ta hanyar Whop, zaka iya shiga cikin tsarin da ke baka damar amfani da videos na wasu manyan creators, ka rika dorawa a social media, sannan ana biyanka gwargwadon views da videos din suka samu.
Whop yana aiki ne a matsayin dandali da ke hada creators da masu tallata content. A wasu shirye-shirye da ke ciki, zaka samu damar shiga communities ko programs da suke baka videos da aka riga aka shirya. Aikin ka shi ne ka dauki wadannan videos ka dorasu a TikTok, Instagram Reels, ko YouTube Shorts.
Yadda ake samun kudi a nan shi ne, idan videos din da ka dora suka samu views masu yawa, ana biyanka gwargwadon yawan mutanen da suka kalla. Wasu programs suna biya ne ta hanyar CPA ko revenue share, wasu kuma suna baka kudi kai tsaye idan ka kai wani matakin views da aka kayyade.
Abu mai muhimmanci a nan shi ne ka fahimci yadda social media ke aiki. Kana bukatar ka rika dora videos akai-akai, ka zabi videos masu jan hankali, sannan ka yi anfani da captions da hashtags masu kyau domin su taimaka wajen kara reach. Idan kayi haka da kyau, zaka iya samun kudin shiga mai kyau cikin lokaci kadan.
Haka kuma, Whop yana baka damar shiga communities inda zaka samu guidance da strategies daga mutane da suka riga suka kware a wannan fanni. Wannan yana taimaka maka ka guji kuskure kuma ka fara ganin sakamako da wuri.
Idan kana son fara samun kudi ta hanyar social media ba tare da wahalar kirkirar content daga farko ba, wannan hanya ta Whop na daya daga cikin hanyoyin da suke da sauki kuma suna da damar kawo riba idan kayi amfani da su yadda ya kamata.
Ga link din : Click Here
