CBN ZAI BADA BASHI GA MATASAN NAJERIYA ‘YAN JAMI’A
Tsarin koyarda sana’o’I a jami’un kasar najeriya ya samo asali ne daga babban bankin najeriya domin tayar da matasa zuwa samun aikin yi da dogaro da kai,wannan shafi na bada wannan bashi me suna TIES [Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme] an bude shi domin matasa masu neman hanyar dogaro da kai.
Babban bankin kasar najeriya [CBN] ne ya samar da wannan tsarin tallafawa dalibai tareda hadin gwiwar makarantun polytechnics da kuma jami’o’I [Universities] domin inganta rayuwar matasan kasar.
A takaice:
- SUNA: Babban bankin najeriya [CBN]
- NAU’I: Undergraduate | Graduate Loan
- KASA: Nigerian
- ADADIN KUDIN: Miliyan dari biyar [500 Million Naira]
- LOKACIN RUFEWA: Ba’a kayyade ba [Not Specified]
Wannan tsari na Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme [TIES] wadda babban bankin kasar najeriya ya fitar na shekarar dubu biyu da ashirin da daya 2021,an tsara shine kadai domin matasa wadanda suke karatun digiri dama wadda suka hada karatun domin samar da aikin yi da bunkasa harkar tattalin arzikin kasar.Wannan tsarin burinsa shine kawo kirkirarrun ayyyuka,wadanda babu su a kasar ta najeriya dan cigaban matasa dama kasar baki daya.
Ga kadan daga ayyukan da za’a inganta:
- Ayyukan sun hadar da inganta kasuwanci,wadda aka dade anayinsa da kuma wadda ba’ama fara shiba ga daliban da suke/suka kammala karatun polytechnics ko universities a wadannan fagagen: Agribusiness-production,processing,storage and logistics;
- Bangaren daya shafi kimiyya da fasahar zamani ta sadarwa [Information technology] -application/software development,business process outsourcing,robotics,data management;
- Akwai ayyukan samar da masana’antu -bangaren nishadi [entertainment],aikin zane [artwork],yada bayanai [publishing],culinary/event management,fashion,photography,beauty/cosmetics;
- Bangaren kimiyya da fasaha kuma sun kunshi [Science and Technology] - medical innovation,robotics,ticketing systems,traffic systems,renewable energy,waste management da sauransu
Abubuwan da ake bukata:
Duk dalibin dayake da sha’awar cika wannan bashin,to dole ne ya zama ya kammala karatu a polytechnics ko kuma jami’a tareda:
- Satifiket [certificate] na digirinsa [BSc/HND/ ko wani abu me kama da haka;
- Takardar shedar kammala bautar kasa [NYSC exemption certificate]
- Kuma kada dalibi ya wuce shekara bakwai da kammala bautar kasa
Duk me son cikawa yazama:
- Ya nema ne a shafin da aka yarda dashi na yanar gizo,kuma ya tabbatar ya bada duk wasu takardu da aka nema domin taimakawa wajen gudanar da lamarin.
- Ya gabatar da kwafi na gaskiya [original copies] lokacin verification [tantancewa] da kuma documentation
- Ya tura takardar proposal na kasuwancin daya ke son farawa
- Ya yarda da duk dokokin da aka zayyana domin kaucewa satar fasahar mutane [plagiarism]
- Yayi amfani da tallafin daya samu ta hanyar data dace
- Gabatar da wurin kasuwanci,da kuma yadda tsarin gudanarwa da kula da kasuwancin yake
- Kula/yarda da duk dokokin da aka gindaya akan tsarin
Reward:
Manyan jami’o’i biyar da polytechnic wadda suke bada kyakykyawan horo na koyan sana’o’i,zasu samu wadannan adadi na bashin gwargwadon iyawarsu:
- First place - N150.0 million
- Second place - N120.0 million
- Third place - N100.0 million
- Fourth place - N80.0 million
- Firth place - N50.0 million
Sannan bada tallafin zai zama a wadannan fagagen ne:
- Agribusiness
- Information technology
- Creative industry, da kuma
- Science and technology
Yadda za’a cika wannan bashin:
Ga duk daliban da suke da sha’awar cika wannan bashin to suyi amfani da wannan link din: