Scholarship ta karatu kyauta a kasar Australia

Scholarship ta karatu kyauta a kasar Australia




Wata jami’a a kasar australia me suna Australian National University[AUN] sun sake sanar da bude

shafinsu na yanar gizo domin daukar dalibai karatun degree na farko daga dukkan sassan duniya,ita wannan scholarship din an bude tane ga daliban da suka cancanta su nemeta me suna Angus Nicholson Honours Scholarship.

Cancantuwar dalibi gameda wannan scholarship din itace ya zama cewa dalibi ya samu admission a daya daga cikin makarantar gaba da sakandare wato jami’a ko kwaleji da sauransu,ko kuma ya ma fara karatu acikinta .


Ita dai wannan scholarship din kyauta ce daga wata jami’ar ta australia me suna ANU bangaren kwalejin lafiya dana likitanci da kuma kwalejin kimiyya na jami’ar.




Wani me suna Mr Jon Nicholson shine ya kirkireta domin tunawa da mahaifinsa wadda ya dade da mutuwa me suna Dr Angus Nicholson wato mahaifi ga shi Mr Jon kenan ,kuma wannan scholarship din zata kashewa kowane dalibi dala dubu goma a kowace shekara ga dalibin daya samu shiga makarantar successfully.

   Cancantar da ake nema ga dalibi:

Ana saran kowane dalibi me sha’awar wannan damar daya bi wadannan ka’idoji domin samun shiga

wannan makaranta ta Australian National University,kamar haka:


• Dole dalibi ya zama dan kasar australia ko kuma na ketare


• Sannan tana bayuwane ga daliban da suka samu admission/suka fara karatu a jami’a ma’ana sun fara digirin farko


• Kuma wannan scholarship din zata bayune ga kwasa kwasan da suke sanannune a makarantar


• Dole dalibi yazama yana da satifiket na gaba da sakandare ko me kama da haka


• Kuma dole ya mallaki transcript na sakamakon GSE [koda kuwa transcript din bada yaren turanci yake ba,to a fassara shi da yaren turancin


• Dole dalibi yazama me ra’ayin karatu,me himma sannan zai iya aiki ba tare da wani ba ,me kyan hali kuma me yazama ya goge wajen yaren turanci


• Dole mutum ya samu cikakiyar offer daga AUN australia


Dole tsarin neman wannan makarantar ya zama bisa doron shaida da shugabanci

Ana da bukatar yaren turanci daga jami’ar ta AUN ga mafi karancin yaren na turanci

                Yadda zaka/ki nema:

Babu wani banbancin neman wannan scholarship din da sauran,kawai dai me son ya cike ya zama dole;


• Ya rubuta wasika ta bayyana ra’ayi rubutacciya zuwa ga Coursework.scholarships@anu.edu.au


• Sannan ka samu mutum biyu a matsayin reference masu kima wadda zasu goyi bayan lamarin ,sannan a hada shi da referee na shi ma’ana wadda zai wuce masa gaba koda wani abu zai taso,shima a tura sakon zuwa

Coursework.scholarships@anu.edu.au


Daga karshe sai a tura duk takardun da ake bukata kafin rufe shafinsu na yanar gizo domin cike sauran tsare-tsaren.

Lokacin rufewa :15 September to 30 November,[a shekara]

Domin nema sai a danna wannan link din dake kasa:

Danna nan

Post a Comment

Previous Post Next Post