Ga masu bukatar karatun bangaren Nursing da midwifery Makarantar lafiya ta Birnin kudu ta bude portal dinta

Ga masu bukatar karatun bangaren Nursing da midwifery Makarantar lafiya ta Birnin kudu ta bude portal dinta




Shahararriyar kwalejin nan ta koyar da kula da marasa lafiya da ungozoma wato[college of nursing

and midwifery] dake birnin kudu a jihar jigawan najeriya sun sanar da sake bude shafinsu na yanar gizo domin daukar sabbin dalibai bangaren ungozoma[midwifery] ga masu bukatar cikawa sai su hanzarta zuwa shafinsu na internet wadda zamu bayyana a kasa.



         Kadan daga tarihin makarantar

Ita dai wannan makaranta me suna School of nursing and midwifery dake birnin kudu a jihar jigawa an kirkireta ne a watan mayu alif dari tara da casa’in da shida[ 1996] a garin birnin kudu,wadda take kilomita arba’in da bakwai 47 km tsakaninta da babban birnin jihar ta jigawa,kuma tana kan titin kano zuwa maiduguri.

Har wayau dai makarantar ta yaye jimillar dalibai ma’ana set ashirin da biyu 22 sets na masu aikin nurse,amma bangaren karatun ungozoma [midwifery] sun fara ne a shekarar dubu biyu da goma 2010 wadda itama daga bisani suka yaye jimillar sets na dalibai har bakwai 7 sets.

Makarantar ta samu sauyin suna daga sunan school zuwa kwaleji a watan mayun dubu biyu da sha biyu 2012 wadda ta shiga jerin dokar jiha [state law NO.7] wadda tsohon gwamnan jihar Alh. [Dr] Sule Lamido .CON ya sabunta ta domin inganta harkar kiwon lafiya a jihar,bugu da kari, an samu karin wata makarantar ta nursing a karamar hukumar hadejia a watan october,2017 a matsayin kwalejin koyar da aikin kula da marasa lafiya [nursing] kamar dai ta karamar hukumar birnin kudu,wadda ita kuma gwamnan jihar na yanzu me suna Alh.Muhammad Badaru Abubakar mni ya samar.

Kwalejin sun samu sahhalewar hukumar [NMCN] ta kasa domin gudanar da wadannan karatun:

1.

General Basic Nursing

2.

General Basic Midwifery

3.

Refresher Course

4.

Post Basic Nursing

College campus

kwalejin suna da wadatattun kayan aiki,ingantattun kayan koyon aiki sannan da lafiyayyun wurin

kwanan dalibai na maza da mata.

RANAR FARA SAYAR DA FORM DIN NA MIDWIFERY:

Kwalejin zasu fara sayar da form din shiga makarantar na BASIC MIDWIFERY [SET 11] na 2021/2022

na zangon karatu daga ranar litinin sha daya ga watan satumba na shekarar dubu biyu da ashirin da daya,zuwa sha daya ga watan nuwamba shekara ta dubu biyu da ashirin da daya.

Monday-11th September,2021 to 11th November,2021

Abubuwan da ake bukata na takardu:

1. Mafi

karancin

credits

guda

biyar

na

sakandare

da

suka

hada

da,

turanci[English],lissafi[Mathematics],Biology,Chemistry da physics wadda kuma be wuce zama biyu ba

na zaman jarabawar SSCE [WAEC or NECO].

Yadda zaka/ki nema:

Ga masu sha’awar cikawa zasuyi rigista ne online ta portal din makarantar:

www.jisconm.edu.ng


Domin karin bayani a tuntubesu ta hanyar aika sakon email ta:

jisconm@gmail.com

Post a Comment

Previous Post Next Post