karatu kyauta ga 'yan Afirka

 

karatu kyauta ga 'yan Afirka

 






Wata kungiya me tallafawa harkar karatun matasa a afirka me suna Ashinaga Africa Initiative wadda aka farata a shekarar dubu biyu da sha hudu 2004.Manufarta shine tallafawa duk wani daya fito daga yankin Afirka domin fadada aikinta wajen tabbatar da bunkasar ilimi ga matasa a kasashen ketare.

Suna tallafawa daliban da suke marayu ne wadda rashin kudin makaranta yasa suka koma gida,saboda matsalolin rayuwa,wannan kungiya tana basu wannan tallafine suma wadda yake dai dai dana masu karatun degree [undergraduate degree].Wannan kungiya ta Ashinaga tana samar da tallafin daya hada da biyan kudin makaranta [tuition],samar da wurin kwana[accomodation],kudin jirgi[travel cost] da kuma sauran bukatu ga dalibai.

Wannan damar ga duk daliban kasashen Afirkane,sannan ga wadanda suka samu wannan damar za'a gayyacesu zuwa mataki na karshe shine jarabawar interview domin tantance iyawar dalibi da kuma hazakarsa akan karatu.

 

Kadan daga ciki

 

· Suna: Ashinaga Africa Initiative

· Wurin karatu: Kasashen ketare

· Nau'in karatu: Secondary school |undergraduate scholarships

· Kasashen da suka cancanta: African countries 

· Lokacin rufewa: January 28,2022

 

Kasashen da suka cancanta

 

Dole dalibi ya zama yana da takardar shedar zama dan kasa,sannan duk kasashen afirka zasu iya neman wannan scholarship din.

 

Abubuwan da ake bukata

 

Domin zama cikakken dalibi ya zama dole:

  •  Ka rasa daya daga cikin iyayenka,ko kuma duka biyun
  •  Ka kammala karatun sakandare,kuma ka karbi satifiket na kammala karatun naka [WAEC/NECO] banda takardar technical ko vocational degree a cikin shekaru biyu na karatu [a kowane lokaci bayan 2nd August 2019,wadda ya hada da na shekarar 2020 da 2021] ko kuma dalibi zai kammala karatun nasa na sakandare sannan ya karbi satifiket dinsa kafin February 28th,2022
  • An haifeshi bayan daya ga watan September 1999
  • Ya zama dalibi yana jin yaren turanci,faransanci ko kuma yaren Portuguese
  • Ya zama dalibi yana daya daga cikin dalibai goma na farko a cikin ajinsu lokacin karatun sakandare
  • Sannan yana da isashshiyar lafiya domin iya karatu a kasashen na waje

 

Takardun da ake bukata

 

Domin neman wannan scholarship din dole dalibi ya shirya mika wadannan takardun:

  •  Photo [style photograph]
  • Katin shedar zama dan kasa ko fasfo
  • Takardar haihuwa ta dalibi
  • Takardar mutuwar mahaifi ko mahaifiya,ko kuma wata shaida da take nuna shi dalibin marayane
  • Reports na dalibi na duk term din na shekara biyu
  • Certificate na kammala karatun sakandare wadda yake dauke da makin da dalibin yaci
  • Wasika ta recommendation daga principal ko malamin makaranta,wannan ya zama yana dauke da email,lambar waya da kuma bayani game da kwazon mutum da kuma halayyar dalibi a makarantar,kuma dole ya zama an saka hannu kuma anyi stamp

 

Yadda ake nema

 

Ita wannan sikolashif tana dauke da matakai guda biyu ne yayin cikewa:

 

Na farko shine dole dalibi zai tabbatar da cancantuwar sa ta hanyar rigistar wannan tsarin.Kadai ga daliban da suka yi rigista ne zasu karbi sakon sheda ta email

 

Sannan na biyu duk daliban da sukayi rigista zasu karbi sakon email tare da link din da zasu bi domin fayyace matsayinsu.

 

Lokacin rufewa

 

Ga daliban da suke daga Lusophone [Angola,Cabo Verde,Guinea Bissau,Sao Tome da kuma Principe da Mozambique] shine Friday 15th October 2021

 

Ga link din:

https://www.ashinaga.org/en/our-work/

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post