Yoneyama Foundation scholarship
Suna: Yoneyama Foundation
Kasa: Japan
Wurin Karatu: Yankin asiya
Nau’in Karatu: Undergraduate|Postgraduate|Masters Scholarships|PhD Scholarships
Kasashen da suka cancanta: Dukkan kasashe
Lokacin Rufewa: Sha biyar ga watan December shekarar dubu biyu da ashirin da daya 2021
A takaice:
Ita wannan kungiya me rajin tallafawa dalibai daga sassan duniya me suna Yoneyama Foundation dake a kasar japan,tana tallafawa dalibai wadanda suke masu kokari/hazaka daga dukkan sassan duniya wadanda suke karatu ko bincike a manyan makarantun koyon karatu na japan din,da kuma zimmar kawo ci gaba a kasarsa dama duniya baki daya.Sannan wannan sikolashif ta Yoneyama an sadaukar ta ne kuma domin tunawa da Mr. Umekichi Yoneyama wani babban dan kasuwa na kasar ta japan din.
Abubuwan da ake bukata:
Ga abubuwan da wannan tsarin sikolashif din ya kunsa:
- Ya zama dama dalibi dama ya riga da ya zabi jami’ar da yake son nema
- Ya zama yana cikin tsarin neman admission din
- Ya zama ya tura wasikar shaidar amincewa [letter of acceptance]
Kadan daga abubuwan da wannan sikolashif din zata kashewa dalibi:
Za’a kashewa dalibi da yen dubu dari biyu da hamsin 250,000 yen a lokacin taron wayar dakai game da harkokin makaranta [orientation] bayan saukar dalibi a cikin kasar ta japan.Sannan daliban da suka samu wannan damar zasu mika takardunsu na receipts.
Daliban da suka samu zasu isa kasar ta japan ne kafin kayyadadden lokacin bada admission,idan har dalibi bai isa kasar ba a watan da aka fara bada wannan sikolashif din to dalibi zai iya rasa duk wata dama,kai!!! a takaice ma dai za’a goge ka daga tsarin bada sikolashif din.
- Undergraduates: 100,000 yen kowane wata
- Masters students: 140,000 yen a kowane wata
- Doctoral students: 140,000 a kowane wata
A shekarar farko kadai na wannan sikolashif din za’a bawa dalibi yen dubu dari hudu 400,000 yen a lokacin daya sauka acikin kasar
Sannan wannan tallafin zaikai har karshen karatun mutum.
Yadda za’a nema:
Lokacin yin interview da kuma sanar da sakamako za’a tura shi ta email ne ta hanyar wadannan lokutan:
1. Mid of February 2022: Tentative selection result
2. End of March 2022: Eligible notice
Idan dalibi yaqi karbar admission a jami’ar daya aka bashi,to zai rasa wannan damar gaba daya ma.
Domin cikewa danna nan:
http://www.rotary-yoneyama.or.jp/english/overseas