Karatu kyauta a kasar Korea (Scholarship)2022
Domin samun cikakkiyar damar karatun zamani da suka hada da engineering,computer science,software,IT da sauran manyan karatun sadarwa dana yanar gizo.
To dama ta samu domin kuwa kamar dai kullum shahararriyar kasar nan me karfin tattalin arziki ta nahiyar asia wato south koreama’ana [korea ta kudu] sun bude shafinsu na yanar gizo domin daukar dalibai daga sassan kasashen duniya da suka hada da nahiyar africa,asia da kuma turai.
Wannan kyakykyawar dama ce ga masu sha’awar cikawa.
Sannan gwamnatin kasar ta korea tana gayyatar duk daliban kasashen duniya kimanin dari da ashirin da biyar 125 a kowace kasa daga cikin kasashe sittin da bakwai 67 wadda suke san karatun degree na farko a kasar ta korean.
Domin zama cikakke ko zababben dalibi ya zama wajibi ya ketare zabi na farko wadda jakadun na kasar ta korean zasu gudanar a kasar ka ko kasar ki ta asali.
A takaice
• SUNA: Korean government scholarship
• WURI: South korea
• NAU’I: Undergraduate student
• DURATION: 4 years
• GLOBAL RANKING: 149
Abubuwan da dalibi zai amfana game da ita:
• Biyan kudin gida kyauta [settlement allowance]
• Biyan alawus kowane wata [monthly allowance]
• Koyar da yaren korea kyauta [korean language training fee]
• Kudin zirga zirga kyauta [round-trip airfare]
• Cikakkiyar kula ga lafiya [medical insurance]
• Biyarda tallafi bayan kammala karatun degree [degree completion grant]
Cancantar Dalibi:
Nationality:
Dole dalibi da iyayensa ya zama basu mallaki katin dan kasa na korea ba.
Idan har dalibi da iyayensa suka mallaki katin dan kasa har biyu[daya wadda yake na korea da kuma na wata kasar daban] to bai cancanta ya nema ba
Dole dalibi da iyayensa su mallaki shedar zama dan kasa mabanbanta.
Sannan iyayen dalibi yazama sun mallaki shedar zama dan kasa na wadda bana gwamnatin korea ba
Sannan dalibi wadda ya mallaki shedar zama dan kasa shi da iyayensa na kasar ta korea to su kai takardunsu na bayanai dayake goyon bayan sun taba zama ko barin kasar daga bisani
Shekarun dalibi:
Dole dalibi yazama kasa da shekaru ashirin da biyar 25 [born after march 1, 1997]
Ire-iren fagagen karatu wadda suke a yanzu:
Dalibi zai nemi daya daga cikin fagagen karatun da yake da sha’awa[department] a jerangiyar
jadawalin karatu wadda bangaren labarai na makarantar ya fitar
Dalibin da yake daga kasashen ketare zai kawai zai iya neman daya daga cikin wadannan na daga bangaren karatu karkashin:Natural science,technology and engineering field
Jadawalin karatu na yamma [night school] da gajeren zangon karatu,karatun yanar gizo[online]dana distant learning wadannan basa cikin tsarin nema ga scholarship din
Muhimmiyar sanarwa:
Koda dalibi ya kasance ya nemi makaranta kafin samun wannan scholarship din ana koyar dashi da yaren turanci,toya tabbatar da cewa zai iya samun canjin yare daga jami’ar ta korea domin kuwa mafi girman yare a kasar shine shine yaren na korea [korean language] wadda ake amfani dashi a duk makarantun kasar
Lokacin rufewa:
Game da rufewa wannan scholarship din sun raba abun zuwa gida biyu kamar haka:
Embassy track: Shine kodai ya zama lokacin budewa da rufewa ya kasance a karkashin sahalewar jakadancin kasar, ko kuma;
University track: Shine ko kuma a karkashin hukumar makaranta,har wayau dai ita wannan damar
zasuci gaba da budeta har zuwa ashirin ga watan goma shekarar nan da muke ciki
Ga masu bukata sai si danna wannan link din dake kasa: