Karatu kyauta a jami'ar sarki Abdul Aziz Saudi Arabia

 Karatu kyauta  a jami'ar sarki Abdul Aziz Saudi Arabia




Suna: King Abdul’aziz university

Wuri: Jeddah [saudi arabia]

Matakin karatu: Bachelor,masters and Ph D

Kirkira: 1967

Nau'in dalibi: Undergraduate and postgraduate

Matsayin makarantar a Duniya: #109 [by QS global world ranking]

DOMESTIC RANK: #01 [Times higher education]

Lokacin gamawa : 4 years[undergraduate],2 years[masters] and 1 year 6 month for Ph D





Kadan daga tarihin makarantar sarki Abdul Aziz dake Saudi Arabia


Jami’ar sarki abdul’aziz wadda take a jedda [saudi arabia] ta kasance makarantar gwamnati wadda aka qirqira alif dari tara da sittin da bakwai 1967 a matsayin makarantar kudi wadda wata kungiya karkashin jagorancin Muhammad Abu Bakr da kuma wani marubuci mw suna Hamza Bogary suka kafa,sannan daga bisani ta koma makarantar gwamnati,kuma itace makaranta ta farko wadda hukumar [the times higher education] ta fitar a jerin manyan jami’o’in yankin larabawa,sannan kuma ta kasance ta dari biyu 200 a jerin manyan jami’o’in duniya.


Kadan daga abinda scholarship din ta kunsa



√ Dole dalibi ya zama yana da cikakkiyar lafiya

√ Sannan makaranta zata bada wadataccen wurin kwana ga dalibai

√ Akwai abinci kullum ga dalibai

√ Biyan alawus riyal dubu hudu 4,000 ga masu karatun Ph D da riyal dubu uku 3,000 ga masu karatun masters saboda fitar da takardun thesis

√ Biyan alawus na liyar dubu biyu da dari bakwai 2,700 na kudin shipping na litattafai bayan kammala karatu

√ Sannan bawa dalibi kudin ticket a kowace shekara 


                 Cancantar dalibi


  Dole dalibi ya cika wadannan ka’idoji:

• Kada dalibi ya wuce shekara talatin da biyar 35 ga masu karatun Ph D,sannan shekara talatin ga masu karatun masters

• Dole dalibi ya zama yana da cikakkiyar lafiya da kuma kyakyawan hali

• Sannan yazama dalibi ba’a taba korarsa a makarantar da ya baro ba,ko kuma aikata wani laifi wadda yaci karo da dokar makarantar

    

 Takardun da ake bukata a gun dalibi

• Curriculum vitae

• Bayanin gaskiya 

• Sannan copy na takardar kammala karatu[certified from saudi embassy]

• Copy na transcript[certified from saudi embassy]

• Sannan wasiqa ta recommendation copy biyu

• Na qarshe shine copy na passport wadda a kalla yakai shekara yana amfani

  

Sannan babu lokacin rufewa

 

Domin karin bayani sai a tuntubi:


Tel.00966126952000

Fax.00966126951281

mail:dgs.scholarships@kau.edu.sa

Websites: https://csc.kau.edu.sa/Default-140073-EN


1 Comments

Previous Post Next Post