Kungiyar KPMG zata bada tallafin karatu ga dalibai yan Nijeriya
Ilimi shine ginshiqin rayuwa da cigaba a cikin al'umma, saboda haka ne ma hukumar KPMG me zaman kanta a nigeria zata dauki daliban da suka kammala karatun sakandare 'yan asalin nigeria zuwa matakin karatu na gaba wato jami'a.
Cancanta
• Dole ne dalibi ya zama ya kammala karatun sakandare a makarantar gwamantin jiha.
• Dole dalibi yazama ya samu qololuwar maki ma'ana(distinction) a darussa biyar a jarabawar neco da waec (turanci da lissafi wajibine)
• Dole dalibi ya samu mafi qarancin maki dari biyu da talatin(230) a jarabawar share fagen shiga jami'a wato (Jamb)
• Dole ya zama dalibi yanada admission letter daga daya daga cikin manyan makarantun gwamnatin tarayyar nigeria
• Dalibi ya zamto dan matakin farko ko na biyu a karatun gaba da sakandare saboda ana lura da su.
Yadda zaku nemi wannan tallafin na kudin karatu daga wannan kungiya
Zaka iya cike scholarship din ta wannan link din;
√ Lokacin rufe yin register: hudu ga watan goma 2021
√ Kasashen da suka cancanta: Nigeria
Wannan kungiyar iya yan kasar Nijeriya zasu bawa wannan tallafin dan haka ma iya yan kasar ne aka amince su cike wannan tallafin
√ Kasar karatu :Nigeria a iya cikin kasar Nijeriya ne kawai za ayi wannan karatun amma ko wacce jami'a mutum zai iya nema.
MATAKI:'Yan gaba da sakandare wadda suka fara karatun jami'a,kwaleji da sauransu
CANCANTUWA: Wajibine dalibi ya kasance ya hada wadannan matakai;
• Ya zama ya kammala karatun sakandare a daya daga cikin makarantun gwamnatin jiha a cikin shekaru biyu.
• Ya zama yanada mafi qarancin makin jarabawar waec ko neco,wato maki biyar da suka hada da turanci da lissafi
• Mafi qarancin makin jarabawar share fagen shiga jami'a wato jamb da maki 230
• Ya zama dalibi yanada admission letter a daya daga cikin manyan jami'o'in gwamnatin tarayyar nigeria
Adadin yawan scholarship din da zasu bayar: Ba qaidi wato ba'a kayyade adadin mutanen da za'a bawa wannan tallafin karatun ba
Yadda zaka/zaki nemi scholarship din : ka/ki tura saqon email zuwa NG-FMKPMGScholarship@ng.kpmg.com tare da suna,adreshin gida,email address,lambar waya
Sannan ka/ki hada wadannan takardun a zipped folder:
• Takardar sakandare (neco,waec)
• Sakamakon takardar jamb
• Takardar admission letter ta makarantar gwamnatin tarayya
• Takardar haihuwa
• Takardar asali
Sannan yayin tura saqon email ka saka wanan code din da zasu tambayeka
KSP2021
° Lokacin rufe rigista 4 october 2021
A qarshe dalibin daya cike daidai abin da ake buqata yanada tabbacin samun wannan scholarship din sannan za'a gayyaceshi