Karatu kyauta a kasar Canada
Canada tana ta biyu daga cikin manyan kasashen dake duniya a girman kasa wacce take gefen Russia tanada yawan mutane saidai bata kai India ba.
Akwai universities da yawa wanda suka kai wajen guda 96 wanda suke cikin biranen kasar daga cikinsu akwai makarantun da suke maraba da bako akan yazo suyi karatu a kasar.
Daga cikin manyan yaren dake kasar akwai turanci ta daya bangaren kuma akwai yaren faransanci. Idan kana son karatu a matsayinka na dalibi hakika ka nema a Canada domin akwai gurare masu yawa kuma masu kyau da dadin karatu.
Mutanen dake Canada sun iya zama da mutane na kowacce kasa a duniya don haka suke da dadin zama sannan akwai ilimi na kimiyya da kuma kasuwanci wanda idan mutum yaje kasar zai koyi daya daga ciki idan har yanada bukatar hakan.
Manyan biranen Canada sune kamar Toronto da kuma Montreal dan haka idan kana son karatu a Canada to ka fara nemansu domin a kidayar da akai ta shekarar dubu biyu da goma sha takwas an rawaito Montreal Canada shine birni na hudu da yan kasashen duniya suka nemi yin karatu a jami'ar birnin yayinda Toronto ta zamo ta goma sha uku.
Kamar yadda kuka sani wasu kasashen suna matukar girmama takardun mutane matukar ba'a kasarsu sukai karatu ba, Nigeria ma na daga cikin wadannan kasashen.
Ga jerin jami'oin daya kamata ku nema a Canada
• Queen’s University
• University of Calgary
• Western University
• University of Waterloo
• Université de Montréal
• McMaster University
• University of Alberta
• University of British Columbia
• McGill University
• University of Toronto
Idan dalibi yana son yin karatun degree dinsa zai iya nema sannan idan ma yayi degree ne yana son yin mastering dinsa ko phD zai iya nema a Canada babu matsala.
Ga Jerin scholarship a Canada na shekarar 2022
√ David Johnston – Lebovic Foundation International Experience Awards in Canada
√ Ubakata Fund for Japanese Students at the University of Toronto in Canada, 2021
√ President’s Scholarship for World Leaders for International Students in Canada, 2021
√ University Entrance Scholarship at Concordia University of Edmonton, Canada, 2021
√ International Undergraduate Student Bursary at the University of Alberta in Canada, 2021
√ General Bursary Program at the University of British Columbia in Canada, 2021
√ TSoM Love Canada Diploma Scholarships for International Students in Canada, 2021
√ VISTA Postdoctoral Fellowships at York University in Canada
√ merit awards for International Students at CEGEP in Canada
√ ESL Graduate Bursary for International Students at University of Saskatchewan, 2021
Idan kuna son nema ga abinda ake bukatar ace kuna dasu
1 acceptance later daga makarantar da mutum yake yi
2 Passport
3 kudi
Danna nan domin cike form
Yadda za kuyi apply din application din
Kusan ya danganta da kalar makarantar da kuka cika ko kuma kuke son su cika amma dai ana son mutum ya kasance ya iya yaren turanci sannan ya samu takardar transcript na makarantar da ya gama da kuma saidar lafiyarsa daga asibiti na tabbatar da Lafiyar mutum sannan ya cike.