Glass

 


GlassWire: App Din Da Zai Nuna Maka Wace App Ke Cin Data a Boye

GlassWire Data Usage Monitor yana daya daga cikin apps mafi anfani ga masu amfani da Android da suke son sanin yadda data dinsu ke karewa cikin sauri.

Mutane da yawa suna sayen data amma kafin su ankara sai ta kare, ba tare da sun san wace app ce ke cin data din ba. GlassWire yana taimaka maka gano duk abin da ke faruwa da internet dinsa a wayarka.

Menene GlassWire?

GlassWire app ne na data monitoring wanda yake nuna maka:

  • Wace app ce ke amfani da data
  • Yawan data da aka kashe
  • Lokacin da apps suke connecting da internet
  • Apps da suke amfani da data a background

Wannan yana taimaka maka ka gane dalilin da yasa data ke karewa da sauri.

Manyan Features Na App Din

GlassWire yana da abubuwa masu anfani sosai kamar:

Data Usage Tracking
Zaka iya ganin yawan MB ko GB da kowace app take amfani da shi.

Real-time Monitoring
Yana nuna maka abin da ke faruwa da internet dinka kai tsaye.

Alerts da Notifications
App din yana gargadinka idan wani app yana cin data sosai ko kuma sabon app ya fara amfani da internet.

WiFi da Mobile Data Monitoring
Yana nuna maka bambanci tsakanin data da WiFi usage.

Yadda Zaka Iya Morarsa

Idan kana amfani da limited data, wannan app zai taimaka maka rage asara ta hanyar:

  • Kashe apps masu cin data a background
  • Gano apps marasa anfani
  • Sarrafa internet usage naka cikin sauki

Haka kuma yana taimaka wa gamers, content creators, da masu amfani da hotspot su san yadda suke kashe data.

Me Yasa Mutane Da Yawa Suke Son Shi

App din yana da:

  • Downloads sama da miliyan 1
  • Rating mai kyau sosai a Google Play
  • Saukin amfani
  • Karamin size wanda baya cika memory

Kammalawa

GlassWire app ne mai muhimmanci ga duk wanda yake son kula da data dinsa da kuma sanin abin da ke faruwa a wayarsa. Idan kana yawan mamakin yadda data dinka ke karewa da sauri, wannan app zai iya taimaka maka gano matsalar cikin sauki.


For Download : Click Here


Post a Comment

Previous Post Next Post