China scholarship

 


Study in China Scholarship: Yadda Zaka Samu Karatu Kyauta a Kasar China

Idan kana neman damar karatu a waje ba tare da wahalar biyan kudin makaranta ba, scholarships na China suna daga cikin mafi sauki da kuma mafi anfani ga dalibai na duniya. Musamman shirin da ake kira Chinese Government Scholarship (CSC), wanda ke daukar nauyin karatu gaba daya ko wani bangare.

Nau’ikan Scholarship a China

Akwai manyan nau’ikan scholarships da zaka iya nema:

Chinese Government Scholarship (CSC)
Wannan shine mafi shahara, yana daukar:

  • Kudin makaranta gaba daya
  • Masauki
  • Medical insurance
  • Tallafin kudi na wata-wata (kimanin RMB 3000 zuwa 3500 ko sama)

Yana da nau’i biyu:

  • Type A: Ana nema ta ofishin jakadanci na kasarka
  • Type B: Ana nema kai tsaye a jami’a

Confucius Institute Scholarship
Wannan yana musamman ga masu karatun harshen Chinese da ilimin koyarwa, kuma yana daukar dukkan kudin karatu.

Provincial ko City Scholarships
Wadannan scholarships suna fitowa daga jihohi ko birane kamar Beijing ko Jiangsu domin jawo dalibai na waje.

ANSO Scholarship
Wannan yana fi karkata ga daliban da ke karatun kimiyya da fasaha.

Manyan Jami’o’i

China na da jami’o’i masu daraja sosai a duniya, kuma sama da jami’o’i 270 suna shiga cikin CSC scholarship.

Abubuwan da ake bukata

Domin neman scholarship, dole ne ka tanadi:

  • Passport mai aiki
  • Certificate da transcript (a fassara zuwa Turanci ko Chinese)
  • Study plan ko research proposal (a kalla kalmomi 800 ga postgraduate)
  • Letters biyu na recommendation daga malamai
  • Medical report (Foreigner Physical Examination Form)
  • Shaidar harshen Chinese (HSK) ko Turanci
  • Acceptance letter daga professor (yana kara chances sosai)

Shekarun da ake bukata

  • Bachelor: kasa da shekaru 25
  • Masters: kasa da shekaru 35
  • PhD: kasa da shekaru 40

Yadda Ake Nema

Hanyar neman scholarship din tana da sauki:

  • Ka zabi jami’o’in da suke bada scholarship
  • Ka cika CSC online application
  • Ka nema a jami’a kai tsaye tare da tura takardu
  • Ka jira sakamako tsakanin June zuwa July

Shawarwari Domin Samun Nasara

Yana da kyau ka tuntubi professor a China kafin ka nema, wannan yana kara yiwuwar a karbe ka. Haka kuma ka rika bin deadlines sosai.

Kammalawa

Scholarship na China wata babbar dama ce ga duk wanda yake son samun ilimi mai inganci kyauta tare da gogewa a wata kasa mai tasowa a duniya.


Don Register: Click Here


Idan baka iya cika application da kanka ba ko kana bukatar taimako, zaka iya tuntubar wannan number domin a taimaka maka:

07080399911

Ka dauki wannan dama da muhimmanci, domin tana iya sauya rayuwarka gaba daya.


Post a Comment

Previous Post Next Post