Al-Yarmouk College of Medical Sciences/ كلية اليرموك الطبية/
Jami'ar koyon ilimin likitanci ta Al-Yarmouk*
An samar da ita a shekarar 2009 a ƙasar Sudan. Jami'a ce wadda take karantar da ilimi mabanbanta na ɓangaren likitanci irinsu Medicine, Medical lab science, Dentistry, Pharmacy da sauransu.
*Motto:* وأما ما ينفع الناس فيمكث في الأرض
*Nau'i:* Private (Ta kudi)
*Shekarar kafuwa:* 2009
*Ɗalibai:* sama da 3,000
*Wuri:* Azhari, Khartoum, Sudan.
*Matsayi:* Jami'ar ita ce ta 30,507 a matakin duniya, ta 1,868 a Afrika, sannan ta 57 a ƙasar Sudan.
*Website:* https://www.yarmoukcollege.edu.sd/
*Email:* contact@yarmoukcollege.com
ILIMIN DA SUKE BAYARWA;
*• Medicine (MBBS):* Shekarun karatu; 6
Kuɗin makaranta; 4,500 dollars (a duk shekara)
*• Dentistry:*
Shekarun karatu; 5
Kuɗin makaranta; 4,500 dollars (a duk shekara)
*• Pharmacy:*
Shekarun karatu; 5
Kuɗin makaranta; 4,000 dollars (a duk shekara)
*• Medical Lab Science:*
Shekarun karatu; 4
Kuɗin makaranta; 3,500 dollars (a duk shekara)
*• Dental Technology (Diploma):*
Shekarun karatu; 3
Kuɗin makaranta; 2,500 dollars (a duk shekara)
Jami'a ce mai inganci wadda hukumar ilimi ta Sudan da Najeriya suka amince da ita. Daga kafuwarta ta yaye likitoci da dama da a yanzu haka suna aiki a asibitocin Najeriya da sauran ƙasashe.
Jami'ar tana dauke da dalibai daga ƙasashe mabanbanta kamar Sudan, Egypt, Najeriya, Saudiyya, Yemen, Qatar, Iraq, Somalia da sauransu.