KARATU A KASAR UKRAINE
Assalamu Alaikum warahmatullah,
Karatu a kasar Ukraine abune wanda kowa zai so yaje yayi, saboda ukraine tana da makarantu manya, kuma tsofaffi sosai, saboda kasar tana da tsohon tarihi.
Akwai jami'u da yawa wadanda zaku iya zuwa a kowani lokaci, dan haka a karshen wannan rubutun zan ajiye muku manyan makarantun da ya kamata kuje.
MUHIMMANCIN KARATU A UKRAINE
Ukraine kasace wacce zakayi karatu cikin jindadi da kwanciyar hankali, domin a kasar babu matsalar tsaro.
A jami'un ukraine ba'a matsawa dalibi kamar yadda muka sani a kasashen mu, amma hakan baya nufin suna kyale dalibansu kawai.
A ukraine babu tsadar rayuwa idan ka hada ta da sauran kasashen turai kamar su England,France da sauransu, dan haka hakan zai taimaka maka sosai gurin yin tattali da adana kudadenka.
Idan ka sauka a ukraine zaka sami hotels na kwana ko kuma ince hostel na dalibai wanda basu da tsada sosai, zaka iya kashe $500-$700 a duk wata tsakanin kudin haya da kuma kudin kashewa duk da kunsan ya danganta da garin da kake, idan a babban burnin kasar kake to dole kudin zaifi haka.
Idan kayi karatu a wannan kasar zaka samu kwarewa sosai wanda baza ka sami irinta ba a wasu kashashen, domin su suna kula da Practical sosai
MUSHKILOLIN KARATU A UKRAINE
Akwai matsaloli da zaka iya haduwa dasu a Ukraine, sune kamar haka
1. Karatu a kasar ba'a daukar shi da muhimmanci kamar irin makarantun America, Amma kuma ba'a raina Makarantunsu.
2. Zaka iya haduwa da matsala kadan ta matsalar tsaro amma 15% kawai
3. Akwai matsala kadan ta nuna ban-banci
4. A Ukraine ana yin wata jarabawa da daliban level 3 medicine, jarabawar tana da wahala saboda da yaran Ukraine ake yinta daga baya sai a fassara ta zuwa English( kamar da Google translate)
5.
TAKADDUN DA SUKE BUKATA
Ana iya amfani da shafukan makarantar domin tura takaddunka a lokacin da aka bude yin rijista. kuna iya aikawa zuwa Ofishin Na musamman wadanda suke Nema dalibai.
1.Shekarun ɗalibi bai zama ƙasa da (17) ba kuma ba zai fi (25) shekaru don matakin jami'a da cibiyar koyar da harshen larabci ko wani abu makamancin haka, da shekaru 30 don matakin Masters, da shekaru 35 dan matakin phd.
3.Dole sai kasarka ta amince da kayi karatu a kasar
4. Dole ka kasance Dalibin da ba 'dan Saudiyya ba.
5. In ka samu a wata makarantar ba zasu baka ba
6. Takaddun shaida dole ne a tabbatar da su daga hukumomin da ke kula da hakan a kasar ka.
7. Certificate na lafiya.





