Karatu A Sudan

 


KARATU A KASAR SUDAN

Tsarin karatu a kasar sudan tsari ne wanda duk wanda ze iya karatu a Nigeria to ze iya yinsa karatun su babu irin takurawa sosai sannan suna kokari a bangaren practical ga courses din da suke da buqatar hakan Sannan yaren da jamiar ku take karatu dashi idan ma turanci ne ko kuma larabci mutum zeyi sauqin koyarsa saboda yawan makarantunsu akwai en kasashe daban-daban sannan malaman su a makaranta basu da girman kai zaka iya wasa dasu da dariya babu wani matsala sannan dukkan abin da baka gane ba zaka iya tambaya a maka bayani.

Tsarin makarantunsu dukka tsarine na semester 2 a shekara kuma karatun da yawan lokuta yakan fara a farkon zafi ya kammala a karshensa saboda basa karatu a sanyi

sannan dake yawancin jamioinsu na kudi ne kuma sannan suna daga cikin hanyoyin samun kudin kasar za kaga private school dinsu suna da dadin karatu kuma muaamalarsu bata da matsalaa.

MUHIMMANCIN KARATU A SUDAN

  • Tsarin iliminsu Yana da Karfi a africa
  • Jamioin su suna ci gaba da wuri saboda akwai gasa
  • Kasace ta tarihi 
  • Shiga da fice a kasar bashi da wahala
  • Sauqin samun admission
  • Sauqin samun visa
  • Kyakykyawar alaqa da Nigeria

MUSHKILOLIN KARATU A SUDAN

  • Garin yana da matuqar zafi
  • Suna da tsadar rayuwa
  • Kafin ka koyi larabci zaka dansha wahala saboda da yawansu basajin turanci
  • Da yawan karatunsu larabci ne musamman jamioin gwamnati

RAYUWA A SUDAN

Rayuwa a sudan tana da matukar sauqi a bangaren mu'amala mutanen sudan mutanene wanda basu da girman kai mazansu da matansu yara da manya donhaka idan kaje baza kaji irin kadaici bah wanda zena saka ka kanajin cewa kamar baka da sakewa

Tinda sudan kasace wanda tattalin arzikinta ya taallaka da kutane masu shigowa donhaka za kaga bako yana da matukar muhimmanci musamman ga hukuma kuma duk wasu abubuwa da zakayi zakagansu cikin sauqi

A bangaren zirga_zirga kuma tsarin su yasha banban da irin wanda muka saba gani a kasashen mu domin su sunfi amfani da wasu dogun motoci wanda suke cemusu mowasalat wadannan gogun motoci sune kamar motocin da suka fi kowanne araha amma kuma akwai kamar su adedeta-sahu da kuma taxi amma wannan suna da tsada.

A bangaren haya kuma suna da tsari biyu akwai tsarin hostel shine wanda zakaga angina hostel na haya dalibai suna zuwa suna kamawa musamman mata zaka iya kama daki kai kadai ko kuma kai da abokanka mafi yawanci zakaga kowanne daki da bandakinsa da kuma kitchen wadannan hostels din sunfi aminchi kuma sun danfi araha

Tssri na biyu kuma shine ka kama gidan haya wanda yana da tsada amma tsadarsa tana banbanta ne da irin unguwar da yake da kuma girmansa sede hostels ya fishi aminchi amma kuma shi yafi hostel enci saboda a hostel zaa iya saka maka wasu dokoki amma shi nan aa.


Donhaka duba da irin wadannan bayanan gaba daya zaka gano ita rayuwa a sudan tana banbantane da kalar wajen da kake da kuma kalar rayuwar daka zabawa kanka Donhaka idqn mutum yana so ya rayu a sudan a cikin babban birninsu wato Khartoum to mafi karancin rayuwa wanda mutum zeyi daga gidan haya zuwa abinchi shine Doller 150. Me dan dadi kuma doller 500 sannan tsaka tsakaiya itace 250

Amma idan a jahohin wajene wanda ba Khartoum to mafi karancin rayuwa zaka iya yinta daga kan Doller 80-100. Medan dadi kuma 300 tsaka tsakiya zata kasance 250.

Wannan banda kudin makaranta iya kudin abinchi kenan da kuma kudin haya sedan abin da ba zaa rasaba na handout Duk wata kenan

JERIN JAMIOIN KASAR SUDAN 

1. Academy of Engineering Sciences Private

2. Ahfad University for Women Omdurman Private

3. Al Fashir University El Fasher Public

4. Nobles College for science and technology Private

5. AlMughtaribeen University Private

6. Al-Neelain University Public

7. Al Zaiem Alazhari University Public

8. Bayan College for Science & Technology Private

9. Blue Nile University Ad-Damazeen Public

10. Canadian Sudanese College Private

11. Dalanj University Dalang Public

12. El Imam El Mahdi University Public

13. Elrazi University Khartoum Private

14. Future University of Sudan Private

15. University of Garden City Private

16. Gezira College for Technology Private

17. Ibn Sina University Khartoum Private

18. International University of Africa Public

19. Karary University Omdurman Public

20. Khartoum College of Medical Sciences Private

21. Mashreq University Private

22. Nahda College Private

23. National College of Khartoum (NCK) Private

24. National College for Medical & Technical Studies Private

25. National Ribat University Private

26. Nile College Bahri Private

27. Nile Valley University Atbara Public

28. Omdurman Ahlia University Omdurman Private

29. Omdurman Islamic University Omdurman Public

30. Open University of Sudan Khartoum Public

31. Public Health Institute Khartoum Public

32. Red Sea University Port Sudan Public

33. Riyadh International College Khartoum Private

34. Hayatt university College Khartoum Private

35. Sudan International University Khartoum Private

36. Sharq El Neal College Khartoum Private

37. Sudan University of Science and Technology Public

38. University of Bakht Al-Ruda Al-Dewaym Public

39. University of Bahri Bahri Public

40. University of Dongola Dongola Public

41. University of Al Qadarif Al Qadarif Public

42. University of Gezira Wad Medani Public

43. University of Kassala Kassala Public

44. University of Khartoum Khartoum Public

45. University of Kordofan Al-Ubayyid Public

46. University of Medical Sciences and Technology Private

47. University of Nyala Nyala Public

48. University of Science and Technology - Omdurman Private

49. University of Sennar Sennar Public

50. University of Shendi Shendi Public

51. University of the Holy Quran and Islamic Sciences Public

52. University of West Kordofan Al-Foula Public

53. University of Zalingei Zalingei Public

54. Wad Medani Ahlia College Wad Medani Non-profit

55. Alyarmouk College Private

56. Riyad International College

57. Delta College

58. Safwa college of science and technology

59. Almanhal college

60. Salam University

Post a Comment