KARATU A KASAR SAUDIA
Jami'oin saudiyya suna burin bawa kowa gurbin karatu kyauta a kasar, musamman ma ga dalibai masu kokari da kuma jajurce wa.
Abinda yasa jami'on saudiyya suka banbanta da sauran:
1. Jami'o'in Saudiyya sun bambanta da ci gaban ilimin su, saboda yawancin jami'o'in Saudiyya suna cikin manyan jami'o'in duniya
2. Jami'o'in Saudiyya suna da kyakkyawan yanayi don binciken kimiyya saboda cibiyoyin bincike na zamani.
3. Yanayin ilimi da tsari a cikin jami'o'in Saudiyya ya banbanta, kamar yadda fitattun ɗalibai daga sama da ƙasashe 200 na duniya ke karatu a jami'o'in Saudiyya
4. Sannan suna da ƙwararrun malamai wadanda suke aiki a jami'o'in Saudiyya, kuma a cikin dukkan fannoni, kuma wadannan malaman suna wakiltar yawancin ƙasashen duniya.
5. Masarautar Saudi Arabiya tana ba da kyakkyawar kulawa ga ɗalibai na ƙasashen duniya, tallafin karatu kyauta, ba tare da kuɗin karatun ba, kuma tare da wasu fa'idodi.
YANDA ZAKA NEMI JAMI'O'IN SAUDIYYA:
Don sauƙaƙe wa kanku, zaku iya yin amfani ta hanyar yanar gizon jami'ar da kuke so ku nema karatu, inda ɗalibai maza da mata za su iya neman duk fannoni na musamman, ban da karatun kiwon lafiya. Certificate din da zaka iya samu a kasar sune kamar haka: (Diploma na Harshen Larabci ga Masu Magana da Wasu Yarukan - Digiri na farko - Babbar difloma - Masters - Doctorate) Duk wanda ya cika ka'idojin da ake bukata tabbas zai samu ba tare da bata lokaci sosai ba.
YANDA ZAKU TURA TAKADDUNKU:
1.Ana iya amfani da shafukan makarantar da domin tura takaddunka a lokacin da aka bude yin rijista.
2. kuna iya aikawa zuwa Ofishin Jakadancin Masarautar Saudiyya.
NAU'O'IN SCHOLARSHIP A SAUDIYA
Nau'o'in scholarship na saudiyya tsari biyu ne:
1.Tallafin cikin gida ga ɗaliban da ba 'yan Saudiyya ba da ke zaune a kasar wadanda suke zama na yau da kullun.
2.Sai daliban kasashen waje wadanda ba sa zaune a kasar
Sikolashif a cikin jami'o'in na Saudiyya iri uku ne:
1. Cikakkiyar sikolaship
2. Wacce zasu dauke maka wani bangaren kai ka biya wani bangaren
3. Sai wacce zaka Biya kuɗi
MUHIMMANCIN KARATU A SAUDIA
Akwai fa'idodi da yawa da zaka iya samu a kasar saudiyya:
1.Kula da lafiyarka data iyalanka wadanda suke zaune a kasar domin ka.
2. Zasu baka kudi a lokacin da kazo.
3. Gurin kwana.
4.Tikiti na tafiya gida hutu duk shekara-shekara, .
SHARUDAN DA ZAKA CIKA:
Daga cikin sharuɗɗa da ƙa'idodin karɓar ɗaliban ƙasashen waje waɗanda ba yan saudiya sune kamar haka:
1.Shekarun ɗalibi bai zama ƙasa da (17) ba kuma ba zai fi (25) shekaru don matakin jami'a da cibiyar koyar da harshen larabci ko wani abu makamancin haka, da shekaru 30 don matakin Masters, da shekaru 35 dan matakin phd.
3.Dole sai kasarka ta amince da kayi karatu a kasar
4. Dole ka kasance Dalibin da ba 'dan Saudiyya ba.
5. In ka samu a wata makarantar ba zasu baka ba
6. Takaddun shaida dole ne a tabbatar da su daga hukumomin da ke kula da hakan a kasar ka.
7. Certificate na lafiya.
8. Baza su dau dalibin da aka taba kora a makarantar kasar.
9. Dole ne mace tazo da muharraminta wato mijinta
MATSALOLIN KARATU A SAUDIA
A kasar saudiyya ba'su yarda da dalibin da baya san karatu ba, kuma basa barin ayi duk abinda ya kwaucewa shari'ar musulumci.
RAYUWA A SAUDIA
Idan ka sami gurbin karatu a saudiyya to a gaskiya baka da wata matsala domin zakana zuwa gida duk shekara sannan zasuna baka albashi duk wata, kuma ba zaka sami matsalar gurin kwana ba.
Sannan zaka iya zuwa masallacin Annabi duk lokacin da baa karatu.
JERIN JAMIOIN KASAR SAUDIA