KARATU A KASAR GHANA
Shi karatu a kasar Ghana kamar karatu ne a irin sauran kasashen mu na Africa kusan babu wani abu da yake banbanta duba da kusancin Aladu da kuma boda da muke dasu, amma kuma idan a bangaran sauqaqawa ne zaka samu yafi Nigeria sauqi saboda duk wanda Ya saba karatu a Nigeria yasan Yanda akejin wahala koma bayan sauran kasan sannan dake kasar tana dogara sosai da en kasar waje da suke zuwa saboda suna samun kudi za kaga ana basu kulawa matuqa ta yanda dalibi ba zeji ya tsani garin ko kuma yana shan wahala bah
MUHIMMANCIN KARATU A GHANA
Turanci
Inde zakayi karatu a Ghana dole zaka koyi turanci saboda a garin ana magana dashi sosai saboda yana daga cikin kasashen Africa da sukafi magana da Turanci
Sauki
Karatunsu babu takurawa ba shan wahala amma kuma ana karatun sosai
Sauri
Babu tsaye tsaye a karatunsu kamar yajin aiki da sauransu donhaka zaka kammala da wuri
MUSHKILOLIN KARATU A GHANA
Raunin certificate
Saboda Yanda aka meda karatu kayan neman kudi za kaga akwai abubuwa marasa kyau da suke faruwa a wasu Jami'oi wanda shiyasa za kaga wasu kasashen suke Rena certificate din wasu Jami'oin kasar amma ba dukkabah.
RAYUWA A GHANA
Rayuwa a kasar kamar rayuwa ne a nigeria bashi da tsada idan ka hadashi da sauran wasu kasashen da ake zuwa karatu na africa irin su sudan zakaga ghana ta fisu sauqi sosai donhaka duk wanda zena iya samun doller 100 ko 200 to ze rayu a ghana cikin rufin asiri tin daga kan kudin haya harma abinchi amma wanda yake samun daga doller 300 abin da yayi sama to wannan ze more sosai.
