KARATU A BENIN

 


KARATU A KASAR BENIN

Shi karatu a kasar BENIN kamar karatu ne a irin sauran kasashen mu na Africa kusan babu wani abu da yake banbanta duba da kusancin Aladu da kuma boda da muke dasu, amma kuma idan a bangaran sauqaqawa ne zaka samu yafi Nigeria sauqi saboda duk wanda Ya saba karatu a Nigeria yasan Yanda akejin wahala koma bayan sauran kasan sannan dake kasar tana dogara sosai da en kasar waje da suke zuwa saboda suna samun kudi za kaga ana basu kulawa matuqa ta yanda dalibi ba zeji ya tsani garin ko kuma yana shan wahala bah 

SAURIN KARATUN BENIN

Wasu da yawa suna zaton cewa irin kasashen da ake zuwa a kammala karatu a karamin lokaci kawai mutum zuwa yake ya bada cin hanci a ragemasa shekaru to ba haka bane kamar yanda kasashenmu suke da tsarinsu to da yawa ma kowacce kasa tana da tsarinta ,  yawancin kasashen da france ta mulka degree dinsu shekara 3 neh misali irin su niger sede a wasu courses ba kamar sauran wanda england ta mulka ba duk da cewa har a na england dinma akwai masu shekara 3 kamar su uganda abin da yake jan wannan saurin shine suna da tsarin da dalibi zeci gaba da karatu a hutu misali kamar a nigeria idan akayi hutun karshen shekara memakon kaje ka huta idan kaga dama zaka iya shiga ajin gaba kai tsaye maana basa hutu shine kawai ,

MUHIMMANCIN KARATU A BENIN

Sauki

Karatunsu babu takurawa ba shan wahala amma kuma ana karatun sosai

Sauri

Babu tsaye tsaye a karatunsu kamar yajin aiki da sauransu donhaka zaka kammala da wuri 

MUSHKILOLIN KARATU A BENIN

Raunin certificate 

Saboda Yanda aka meda karatu kayan neman kudi za kaga akwai abubuwa marasa kyau da suke faruwa a wasu Jami'oi wanda shiyasa za kaga wasu kasashen suke Rena certificate din wasu Jami'oin kasar amma ba dukkabah.

RAYUWA A BENIN

Rayuwa a kasar kamar rayuwa ne a nigeria bashi da tsada idan ka hadashi da sauran wasu kasashen da ake zuwa karatu na africa irin su sudan zakaga ghana ta fisu sauqi sosai donhaka duk wanda zena iya samun doller 100 ko 200 to ze rayu a ghana cikin rufin asiri tin daga kan kudin haya harma abinchi amma wanda yake samun daga doller 300 abin da yayi sama to wannan ze more sosai.

JERIN JAMIOIN KASAR BENIN






Post a Comment