2013

 


WAMR: Yadda Zaka Ga Deleted Messages a WhatsApp da Sauran Apps

WAMR: Reveal deleted messages! yana daya daga cikin apps mafi shahara da mutane suke amfani da shi domin ganin messages da aka goge a WhatsApp da sauran chat apps.

Sau da yawa mutum zai turo maka message sannan ya goge shi kafin ka gani, hakan yana sa mutane da yawa su shiga tunani akan me aka rubuta. WAMR yana kokarin warware wannan matsala ta hanyar adana notifications na messages kafin a goge su.

Yadda WAMR Ke Aiki

App din yana anfani da notification history na wayarka domin yin backup na messages da suke shigowa. Da zarar wani ya goge message, WAMR zai baka notification sannan ya nuna maka abinda aka goge.

Wannan yana aiki ne saboda app din yana adana bayanan messages daga notifications kafin a cire su.

Abubuwan Da WAMR Zai Iya Dawowa

Ba messages kadai ba, WAMR yana iya kokarin dawo da:

  • Hotuna
  • Videos
  • Voice notes
  • Audio
  • GIFs
  • Stickers

Idan media din ya gama downloading kafin a goge shi, akwai damar app din ya adana shi.

Karanta Messages Ba Tare da Blue Tick Ba

Daya daga cikin abubuwan da mutane suke so a WAMR shi ne yana baka damar karanta messages daga notification backup ba tare da sender ya ga blue ticks ba.

Wannan yana kara privacy yayin amfani da chats.

Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani

Domin app din yayi aiki da kyau:

  • Notifications dole su kasance a kunne
  • Kada a hana app din aiki a background
  • Internet mai kyau yana taimakawa wajen adana media files

Abubuwan Da WAMR Baya Iya Yi

Akwai wasu limitations:

  • Ba zai iya dawo da messages da aka goge kafin ka install app din ba
  • Wasu phones ko Android versions na iya rage yadda yake aiki
  • Idan notification bai iso ba, app din ba zai iya adana message din ba

Tsaro da Privacy

WAMR yana adana bayanai ne a cikin wayarka kawai. Wannan yana nufin chats dinka basa tafiya zuwa server na wani daban.


For Download : Click Here

Iphone: Click Here

Kammalawa

Idan kana son ganin deleted messages ko media da aka cire a WhatsApp da sauran chat apps, WAMR yana daya daga cikin apps mafi anfani da zaka iya gwadawa.

Yana taimaka maka rage mamaki da kuma baka damar ganin messages kafin su bace gaba daya.


Post a Comment

Previous Post Next Post