DualTake Cam: Ka Dauki Video Daya, Ka Samu Formats Biyu Lokaci Guda
Idan kana yin content a social media, ka san yadda yake wahala ka rika gyara video domin ya dace da TikTok, Instagram, da YouTube daban-daban. Amma yanzu akwai mafita mai sauki ta hanyar DualTake Cam.
Wannan app yana baka damar daukar video sau daya kawai, amma ya baka shi a portrait da landscape lokaci guda. Wannan yana nufin ba sai ka sake recording ko editing mai wahala ba.
Yadda App Din Ke Aiki
Da zarar ka bude app din, zaka iya fara recording kamar yadda kake yi da camera na waya. Amma abin ban mamaki shi ne, yayin da kake daukar video daya, app din yana kirkirar formats biyu a lokaci guda.
Wannan yana da anfani sosai ga wadanda suke posting a dandamali daban-daban, domin wasu suna bukatar tsaye (portrait), wasu kuma kwance (landscape).
Manyan Features Na DualTake Cam
Daya daga cikin manyan abubuwan da app din ke bayarwa shi ne dual format recording, wato video daya amma yana fitowa a siffofi biyu. Haka kuma yana da saukin amfani, ba sai ka kware sosai a editing ba kafin ka anfani da shi.
App din kuma yana inganta quality na camera domin ka samu video mai kyau da tsabta. Sannan yana da sauri kuma baya daukar lokaci wajen processing.
Yadda Zaka Iya Morar App Din
Idan kai content creator ne, wannan app zai rage maka wahala sosai. Maimakon ka dauki video sau biyu ko ka shiga editing mai wahala, zaka iya amfani da DualTake Cam ka gama komai lokaci guda.
Haka kuma zai taimaka maka ka rika posting cikin sauri da kuma consistency, wanda yake da muhimmanci wajen samun views da followers.
A takaice, DualTake Cam app ne da zai saukaka rayuwar duk wanda yake aiki da video, musamman masu social media, domin yana rage lokaci, wahala, kuma yana kara ingancin content dinka.
For Download: Click Here
