Dub.ai da “One Million Prompters”: Babbar Dama Ta Koyon AI da Samun Kwarewa
A yau, duniya tana komawa kan Artificial Intelligence cikin sauri, kuma wannan ya kawo sabuwar dama ga duk wanda yake son koyon yadda ake anfani da AI domin samun kudi da kwarewa. Dub.ai yana daga cikin dandamali da ke taimakawa wajen wannan tafiya.
Menene “One Million Prompters”?
“One Million Prompters” wata babbar shiri ce da aka kaddamar a Dubai domin koyar da mutane yadda ake amfani da AI ta hanyar prompt engineering. Wannan shiri yana da burin horar da mutane miliyan daya cikin shekaru uku.
An fara wannan shiri ne domin karfafa amfani da AI a duniya, musamman ta hanyar koyar da yadda ake rubuta umarni (prompt) da zai sa AI ya baka sakamako mai kyau.
Mecece Prompt Engineering?
Prompt engineering wata fasaha ce da ke koyar da yadda zaka rubuta tambaya ko umarni ga AI yadda zai baka amsa mai inganci. Wannan na iya hada da:
Kirkirar content
Samar da ideas
Warware matsaloli masu wahala
Rubuce-rubuce na kasuwanci ko ilimi
Yadda Wannan Zai Amfaneka
Idan ka koyi prompt engineering, zaka iya anfani da AI wajen:
Kirkirar videos da content cikin sauki
Samun hanyoyin kasuwanci
Inganta aikinka na yau da kullum
Samun sabbin damammaki a aikin online
Wannan shiri yana ba mutane horo, takardar shaida (certificate), da kuma kwarewa da ake bukata a wannan zamani.
Dalilin Da Ya Sa Wannan Dama Ta Musamman Ce
Wannan initiative yana daya daga cikin mafi girma a duniya, kuma yana bin sahun wani shiri mai suna “One Million Arab Coders” wanda ya taimaka wa mutane da dama su koyi coding.
Haka kuma, yana da alaka da gasar duniya ta prompt engineering da aka yi a Dubai, inda dubban mutane daga kasashe daban-daban suka shiga.
Kammalawa
Idan kana son shiga duniya ta AI da kuma samun kwarewa mai anfani a nan gaba, wannan dama ta “One Million Prompters” tana da matukar muhimmanci.
Yanzu lokaci ne da zaka fara koyon yadda ake anfani da AI, domin wannan ilimi zai iya bude maka hanyoyi masu yawa na samun kudi da cigaba a rayuwa.
For Resigter : Click Here
