223322

 


Nau’ikan Karatu a Masarautar Saudi Arabia: Cikakken Bayani Ga Dalibai

Idan kana da burin karatu a Saudi Arabia, yana da muhimmanci ka fahimci nau’ikan damar da ake bayarwa. Wannan bayanin zai taimaka maka ka gane yadda tsarin karatu da scholarships suke aiki, da kuma yadda zaka anfani da su.

Cikakken Scholarship (Fully Funded)

Cikakken scholarship shi ne gurbin karatu da dalibi namiji ko mace daga kasashen waje ke samu domin yin karatu a jami’o’i ko manyan makarantu a Saudi Arabia ba tare da biyan kudin karatu ba.

Gwamnatin Saudi Arabia na bayar da wadannan scholarships domin karfafa ilimi da kuma hada kan al’ummomi ta hanyar musayar al’adu. Wannan dama ce mai girma ga daliban da suke son cigaba da karatu a jami’o’in kasar.

Wannan scholarship yana daukar dukkan kudin karatu da kuma wasu muhimman abubuwa da suka hada da hidimomin jami’a. Haka kuma ana ba dalibai tallafin kudi domin su samu saukin rayuwa.

Ana zabar wadanda zasu amfana da wannan scholarship ne bisa cancanta kamar:

  • Kwarewa a karatu
  • Hazaka da basira
  • Kwarewa a fannoni daban-daban

Dalibi dole ne ya gabatar da takardu kamar certificates da kuma shaidun makaranta.

Saudi Arabia na bayar da damar karatu a fannoni da dama kamar:

  • Kimiyya
  • Injiniya
  • Ilimin dan Adam
  • Fasaha
  • Ilimin zamantakewa

Daliban da suka samu wannan scholarship suna da damar fahimtar al’adun kasar da kuma hulda da dalibai daga kasashe daban-daban.

Fa’idodin Scholarship

Daliban da aka karba suna samun:

  • Kula da lafiya su da iyalansu idan sun zo tare
  • Tallafin kudi lokacin zuwa
  • Masauki
  • Duk wasu hakkoki irin na sauran dalibai
  • Tikitin jirgi na shekara-shekara bisa ka’ida

Scholarship Na Rabi (Partial Scholarship)

Wannan ma scholarship ne da ake baiwa daliban kasashen waje domin karatu a Saudi Arabia, amma ba lallai ne ya dauki dukkan kudin karatu ba.

Ana bayar da shi domin karfafa ilimi da hadin kai tsakanin al’ummomi. Dalibai suna bukatar su nema tare da gabatar da dukkan takardun da ake bukata kamar yadda ake yi a cikakken scholarship.

Wannan ma yana taimakawa wajen:

  • Samun ilimi mai kyau
  • Kara kwarewa
  • Inganta fahimtar juna tsakanin kasashe

Visa Na Gajeren Lokaci (Short Term Visa)

Ana bada wannan visa ne domin:

  • Karatu na dan lokaci
  • Training
  • Shiga short programs
  • Musayar dalibai

Lokacin visa:

  • Watanni 6
  • Ana iya kara watanni 6

Sharudda:

  • Shekaru 16 zuwa sama
  • Passport mai aiki akalla watanni 6
  • Samun admission daga makaranta a Saudi
  • Shaidar cewa zaka iya daukar nauyin kanka ko mai daukar nauyi
  • Izinin waliyyi ga wadanda basu kai shekara 18 ba

Visa Na Dogon Lokaci (Long Term Visa)

Wannan visa ana amfani da shi domin:

  • Karatu mai tsawo
  • Aiki
  • Bincike

Ya dace da:

  • Bachelor
  • Masters
  • PhD

Lokacin visa:

  • Shekara 1
  • Ana iya sabunta shi duk shekara

Sharudda:

  • Shekaru 16 zuwa sama
  • Passport mai aiki
  • Admission daga jami’a
  • Shaidar kudi ko mai daukar nauyi
  • Izinin waliyyi ga kasa da 18
  • Rahoton lafiya
  • Insurance
  • Kwarewa a harshen karatu (sai dai idan Arabic zaka karanta)

Karatu Da Kudi (Paid Study)

Wannan nau’i ne na karatu inda dalibi zai biya kudin karatu da kansa.

Ana zabar dalibai bisa cancanta, kuma dole ne su gabatar da takardunsu kamar certificates da sauransu.

Fa’idar wannan tsarin:

  • Samun ilimi mai inganci
  • Hada kai da dalibai daga kasashe daban-daban
  • Kwarewa da gogewa a rayuwa

Kudin karatu yana bambanta daga jami’a zuwa jami’a, kuma ana iya dawo da wasu kudade idan dalibi ya janye ko ya dage karatu bisa dokokin makaranta.

Kammalawa

Saudi Arabia tana daya daga cikin kasashen da ke baiwa dalibai dama mai girma wajen karatu. Ko dai scholarship ne ko kuma karatu da kudi, duk suna da anfani sosai.

Idan kana da burin samun ilimi mai kyau tare da gogewa a wata kasa daban, wannan dama ce da ya kamata ka duba da kyau ka kuma anfani da ita yadda ya kamata.





For Registration : Click Here


Ga lambar Me cape : +2347080399911


Post a Comment

Previous Post Next Post