Hacettepe University
Suna : Hacettepe University
Kasa : Turkey
Nau-i : Ta gwamnati
Courses : 16
Kirkira : 1954
Jerin kasa : null
Scholarship : Akwai
Jerin Duniya : null
Yaren karatu : English
Dalibai : 49582
Gari : Ankara, Turkey
Takaitaccen Tarihin makarantar
Tarihin Jami'ar Hacettepe an kirkireta ne a lokacin da aka kafa Cibiyar Kula da Lafiyar Yara a ranar 8 ga Yulin 1958, da kuma ƙaddamar da Asibitin yara na Hacettepe wanda Farfesa Dr. İhsan Doğramacı ya kafa. A shekarar 1961 aka bude Makarantar Kimiyyar Kiwan lafiya da bangarorinta na Nursing, Technology Medical, Physical Farrapy and Rehabilitation da Nutrition, dukkansu suna Cibiyar Kula da Kiwon Lafiyar Yara.

Bayani
Jami'ar Hacettepe babbar jami'a ce a jihar ta Ankara, Turkiyya. jami'ar tana matsayi na 1 tsakanin jami'o'in Turkiyya tare da makarantun likitanci. Jami'ar na da manyan makarantu biyu. Na farko yana cikin tsohuwar garin Ankara. na biyu kuma shine Beytepe Campus, wanda yake kilomita 13 (8 mi) daga tsakiyar gari. Kwalejin Beytepe ta rufe 6,000,000 m2 (600 ha; 1,483 acres) na ƙasar kore da dazuzzuka, kuma tana ɗaukar nauyin ilimin Kimiyya da fasaha kyauta.
Jami'a ce mai inganci wadda hukumar ilimi ta Turkey da Najeriya suka amince da ita.
Jami'ar tana dauke da dalibai daga ƙasashe mabanbanta kamar Sudan, Egypt, Najeriya, Saudiyya, Qatar, Somalia da sauransu.
FACULTY DA COURSES ;
Faculty of Medicine
Medicine (Turkish Medium)
Medicine (English Medium)
Faculty of Medicine at Kastamonu
Faculty of Pharmacy
Faculty of Science
Actuarial Sciences
Biology
Chemistry
Mathematics
Statistics
Schools Edit
School of Foreign Languages
Basic English Division
English Preparatory Division
German Preparatory Division
French Preparatory Division
School of Sports Science and Technology
Institutes Edit
Atatürk Institute for Modern Turkish History
Institute of Child Health
Institute of Population Studies
Institute of Pure & Applied Sciences
Institute of Social Sciences
Institute of Health Sciences
Institute of Fine Arts
Institute of Public Health
Institute of Neurological Sciences
Institute of Nuclear Sciences
Institute of Oncology
Institute of Turkology Research
Environmental Research and Application Center (ERAC)
Vocational schools Edit
Bala Vocational School
Hacettepe Vocational School
Health Services Vocational School
Polatlı Health Services Vocational School
Polatlı Technical Science Vocational School
Social Sciences Vocational School
SHARRUDAN KARATU A KASAR TURKIYYA
Daliban da ke son samun tallafin karatu na gwamnatin Turkiyya, turkiye burslari, dole ne su cika sharuɗan da ƙungiyar malanta ta tsara.
Sharuddan sune kamar haka
Mafi qarancin abinda ake bukata awajan masu digiri na farko su sami makin Bakaloris da ya kai 70%
75% don masu neman digiri na biyu da na uku
mafi karancin abinda ake nema a wajan masu neman courses na harkar lafiya su likitan hakori ya zama 90%
Masu neman Digiri na farko dole ya kasance kada shekarunsu ya gaza 21. masu neman Masta kuma kada shekarunsu ya gaza 30.
masu neman Doktora kuma kada ya gaza 35
suna bawa kowa ya nemi scholarship dama amma banda dam kasar ta Turkiyya ko wanda keda shedar zama dan Turkiyya.
FA'IDOJIN KARATU A KASAR TURKIYYA
Ga duk dalibin da ya samu gurbin karatu a wannan kasar ta Turkiyya yana iya samu wasu fa'idoji da dama kamar haka :
Na farko baze biya kudin makaranta ba har ya kammala.
Na biyu Za'a bawa lafiyarsa cikakkiyar kulawa.
Na uku A duk wata dalibin digiri zena daukar albashin Lera ta Turkiyya kimanin 700, Dalibin masta kuma 950, na Doktora kuma 1400.
Na hudu Samar da gida ga daliban masta ko kuma a baka kudin hayan gida.
Na biyar Zaka koyi yaren Turkiyya na tsawon shekara guda.
Na shida za'a saya maka tikiti na zuwa gida hutu dana dawowa a karshen shekara.
Na bakwai zaka samu duk wani abu da dalibin Turkiyya jami'ar take bashi, irinsu katin jigilar kaya, katin ragin kaya da katin shiga gidajen tarihi.
Bayan wadannan fa'idoji da aka ambata daliban da suke digiri na farko zasu iya shiga makarantar koyon turanci kyauta na tsawon shekara idan kwas dinsu yana bukata
TAKARDUN DA ZAKA NEMI SCHOLARSHIP DASU
Duk masu neman izinin Scholarship na Turkiyya dole ne su gabatar da takaddun kamar haka.
1. INGATACCEN KATIN FASFO
2. HOTON DA YA DACE WANDA ZE FIDDA DUK KAMANNINKA
3. SAKAMAKON JARRABAWAR KASA DA KASA GA DALIBAN DA BASUDA TAKARDAR GAMA KARATU
4. TAKARDA SHAIDAR KAMMALA KARATU.
5. BAYANIN SAKAMAKO( RESULT)
6. Sakamakon jarrabawar ƙasa da ƙasa (GRE, GMAT, DELF, YDS, YÖS ... da sauransu. Idan ɗaliban jami'a da shirye-shirye suka buƙata)
Tsarin bincike da misali na rubutaccen aikinku (don masu neman PhD kawai).
Wasikun SAUTI
Ba a buƙatar lasisi da takaddun shaida na duniya don yawancin manyan. Dalibai za su iya neman tallafin karatun Turkiyya ba tare da TOEFL ko takardar shaidar IELTS ba.
Kuna iya haɗa duk wasu takardu waɗanda zasu iya taimaka muku don haɓaka damar ku na karɓar ku a cikin tallafin karatu na Turkiyya, kamar irinsu takardun karbar horo da makamantansu.
DOMIN TUNTUBAR JAMI'AR KAI TSAYE
Wuri: Istanbul, Turkey
Website: http://www.hacettepe.edu.tr
Lambar waya: +90(312) 311-99-92
